M
MINING HUNTER°
@Thqsqi_pqgRlZDdk3.0K подп.
163просмотров
5.5%от подписчиков
29 марта 2026 г.
Score: 179
Updating na password yana da matuƙar muhimmanci sosai domin yana ƙara kare account ɗin ka daga barazana. Abin takaici, mafi yawancin mu ba mu damu da sabunta password ɗin mu ba. Wasu ma har sukan yi amfani da password iri ɗaya a dukkan account ɗin su. Wannan babban kuskure ne, domin idan aka gano password ɗaya, zai zama mai sauƙi a shiga duk sauran asusunka. Kamar yadda masu ƙirƙirar apps ke sabunta tsarin app ɗin su lokaci zuwa lokaci, haka ya kamata kai ma ka riƙa sabunta password naka akai-akai. Ba password kaɗai ba idan aka baka damar sabunta hoton ka ko bayanan ka (profile), ka riƙa yin hakan. Wannan yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sahihancin bayanan ka. Sau da yawa, mutum kan yi amfani da tsohon hoto ko tsoffin bayanai na tsawon lokaci. Idan aka zo yin wani abu mai muhimmanci, sai a ga bambanci tsakanin tsohon bayanin da halin da ake ciki yanzu. Saboda haka, duk wani app da kake amfani da shi  musamman na banki, exchanger, da makamantansu ka tabbata kana ba su cikakken tsaro. ✍️ Mining Hunter
163
просмотров
1038
символов
Нет
эмодзи
Нет
медиа

Другие посты @Thqsqi_pqgRlZDdk

Все посты канала →
Updating na password yana da matuƙar muhimmanci sosai domin — @Thqsqi_pqgRlZDdk | PostSniper